Daga Isma'eel Abba Tangalashi
Tsohon dan wasan Nigeria ta yan kasa da shekaru 23 kuma wanda ke taka ledarsa a kungiyar Kwallon kafa ta Ostersunds FK dake kasar Sweden, Alhaji Gero, yayi Alkawarin haskakawa a wasan da kungiyar sa zata kara da kungiyar Kwallon kafa ta Arsenal da misalin karfe bakwai a yammacin Alhamis din nan.
Dan wasan mai shekaru 24 ya haskaka a wasannin rukuni inda ya zura kwallaye guda uku a gasar ta Europa.
"Wasan da zamu kara da Arsenal yana da muhimmanci a gare ni da ma kungiyar mu ga baki daya.
"Arsenal babbar kungiya ce mai dumbin tarihi da tarin magoya ba.
"Zamu yi iya kokarin mu domin samun nasara a wannan gasa. A cewar Gero.
Ostersunds FK dai ta fito ne daga rukunin da ya kunshi kungiyo irin su Athletco Bilbao, Hertha Berlin da kuma kungiyar Kwallon kafa ta Zorya.
Sai dai babban burin Gero bai wuce samun adu'a daga magoya bayan sa ba. Inda ya ce, "Ina Alfahari da magoya baya na kuma ina bukatar adu'ar su a wannan gagarumin wasa dake gaban mu.
Wannan wasa shine mafi girma a tarihin kungiyar Kwallon kafar ta Ostersunds, wacce aka kirkire ta a Shekarar da Mai horar da Arsenal, Arsene Wenger ya karbi ragamar horaswa a Arsenal a shekarar 1996.
Comments
Post a Comment