Isma'eel Abba Tangalashi
Shugaban hukumar Kwallon kafa ta Jihar Kano kuma member a hukumar zartarwa ta hukumar Kwallon kafa ta Kasa, NFF kuma Shugaban nada Alkalan wasa ta kasa, Alhaji Sharu Inuwa Rabiu Ahlan, ya gargadi Alkalan wasa da shuwagabanni kungiyoyi da su daina kawo rudani a harkar Alkalanci da ke sauya sakamakon wasa a gasar Primiyar Nigeria.
Ahlan ya bayyana hakan ne a yayin da yake zantawa da gidan radio Aminci mita 103.9 kai tsaye ta wayan tarho.
Galadimar Kwallon kafar Nijeriayar ya bayyana bacin ransa inda ya ce hukumar baza ta kyale wani ya lalata shirin da ta dade tana yi na ganin ta kawo gyara a bangaren Alkalanci da ci gaban Kwallon kafa a kasa baki daya ba.
"Zamu sa kafar wando daya da duk wani Alkalin wasa ko shuganin kungiyoyi dake kawo mana cikas a fagen gudanar da harkar Kwallon kafa.
"Muna duba yiwuwar shigowa da hukumar EFCC domin rage kurakuren da almundahana da ake samu a Kwallon kafa, a cewar Ahlan.
Ahlan ya bayyana Kwallon kafa a matsayin abu daya tilo dake kawo hadin kai a kasa inda ya kara da cewa shi da mataimakan sa zasu yi duk mai yiwuwa domin tsabtace harkar.
Idan ba a manta ba hukumar gudanar da gasar Primiyar Nijeriya ta dakatar da wasu Alkalan wasa da sukayi Alkalanci a wasannin mako na 14 na gasar bayan nuna rashin kwarewa.
"Ina kira ga Alkalan mu da babbar murya da su san cewa yanzu ba da bace. Dole sai sun kasance masu juriya da gaskiya kafin a basu wasa.
Comments
Post a Comment