Kungiyar Kwallon Kafa Ta Lobi Stars Ta Tsinci Dami A Kala


Daga Isma'eel Abba Tangalashi



An dakatar tare da nada Kungiyar Kwallon Kafa ta Lobi Stars dake garin Makurdi a matsayin wacce ta lashe gasar primiyar Nigeria na kakar 2017/2018 bayan wasannin 24 kacal.


Hakan ya ba Kungiyar damar zama kungiya daya tilo da zata wakilci kasar nan a gasar zakaru ta nahiyar Afirka a Kaka mai zuwa.


An cimma matsayar hakan ne a jiya yayin taron gaggawa da hukumar shirya gasar ta primiya tayi da Shuwagabanni kungiyoyin gasar 20.


Hakazalika, babu kungiyar da zata fada ajin kwararru inda akesa ran hada Kungiyoyin primiyar 20 da karin 4 da zasu hauro daga ajin na gajiyayyu domin fafatawa a kakar shekara ta 2018/2019.


Jimillar kungiyoyi 24 ne zasu fafata a gasar mai zuwa inda za a raba su zuwa rukuni 2 mai dauke da kungiyoyi 12 kowanne.


Hukumar Kwallon Kafar ta Kasa nff tasha fama da rigingimu na shugabanci wanda ya kusa kawo karshen harkokin Kwallon Kafa a cikin kasar baki daya.


Kungiyar Kwallon kafar ta Lobi ke jan ragamar gasar da maki 43 sai Akwa Utd a matsayi na 2 da maki 41 a yayin da kungiyoyin Kano Pillars da Enyimba ke mataki na 3 dana 4 da maki 38 kowannen su.


Dukannin sauye sauyen zasu fara aiki ne bayan sahalewar hukumar Kwallon Kafa ta Kasa nff da ake sa ran zata fitar bayan wani tarron gaggawa da zatayi da misalin karfe 12:30 na daren yau Juma'a, 30 ga Watan Agusta, 2018 a cewar Shugaban kungiyoyin primiya na kasar nan, Isaac Danladi.


Ana sa ran fara gasar kakar shekara ta 2018/2019 ne a watan numbar wannan shekarar sannan a Kammala a Watan mayun shekara mai zuwa

Comments