Daga Isma'eel Abba Tangalashi
Bisa ga dukkan alamu Nijeriya ta tsallake rijiya da baya dangane da kora daga cikin harkokin da suka shafi tamaula da hukumar kwallon Kafa ta duniya, FIFA taso yi mata a daidai karfe 12 na wannan rana ta Litinin.
Gwamnatin Tarayya ce ta kawo karshen wannan batu da ya jima yana kawo tarnaki cikin shugabancin hukumar ta NFF.
Gwamnatin Tarayyar dai ta sanar da hukumar Kwallon Kafar ta duniya, FIFA cewa, Shugabancin Amaju Melvin Pinnick shine halastacce inda ta kara da cewa zatayi duk mai yiwuwa tare da biyayya ga dukkanin dokin dake cikin sadarorin hukumar ta FIFA domin kare afkuwar hakan a gaba.
A makon jiya ne dai hukumar ta FIFA ta bada sanarwar zata iya dakatar da kasarnan daga shiga cikin harkokin kwallon kafa da misalin karfe 12 na wannan rana ta Litinin agogon Nijeriya muddin hukumomin kasar nan suka cigaba da bujirewa dokokin ta.
Idan ba a manta ba, rikicin shugabancin na NFF ya tsayar da harkokin kwallon kafa na lig lig da aka saba gudanarwa a cikin gida.
Cris Giwa, wanda ake ganin dan lele ne ga Ministan Wasanni kasar, Barista Solomon Dalung, yasha ikirarin shine shugaban hukumar, yayin da a gefe guda Amaju Melvin Pinnick da Mukarrabansa ke nanata cewa sune halartattun shuwagabannin hukumar ta NFF.
Kawo yanzu dai hukumar ta FIFA bata ce uffan akan wannan batu ba koda kuwa a shafukanta na Twitter da yanar Gizo.
A safiyar wannan rana ta Litinin, hotunan matasan kasar nan ne keta yawo a kafafen sada zumunta rike da kwalaye me dauke da rubutu daban daban, inda a ciki suke kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da ya kawo musu agajin gaggawa.
www.tangasports247.blogspot.com
Comments
Post a Comment